Tsohon fira ministan Moroko ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce kashin bayan gwagwarmaya a Zahiri
Tsohon fira ministan kasar Moroko kuma babban sakataren jam’iyyar Adalci da ci gaban kasar Abdul-Ilah Ben Kiran, ya jaddada cewa: Ba zai yiwu mu iya musun cewa Iran ita ce ginshikin gwagwarmaya a yau ba, bisa gaskiyar zance, kuma ita ce a sahun gaba wajen goyon bayan ‘yan gwagwarmaya da karfafa su wajen kalubalantar yahudawan sahayoniyya a duniya.
Ben Kiran ya yi tambaya game da irin rawar da musulmi da larabawa suke takawa wajen tallafawa al’ummar Falastinu da kuma dakatar da laifukan kisan kiyashi da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a Gaza! yana mai cewa: Su ‘yan Ahlul-Sunna waj-Jama’a ne da suke wakiltar kashi 90 cikin 100 na al’ummar musulmi, kuma babu matsala Iran ta kasance tana da rawar gani, amma su kuma wane rawa suke takawa?
Tsohon Fira ministan Moroko ya zargi gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da rashin tausayi da gudanar da dabi’un dabbobi. Yana gargadin cewa: Bai dace su dauki duk wani matakin sadarwa ko haɗin kai da haramtacciyar kasar Isra’ila ba, kuma dole ne a kan kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta raba gari da ‘yan sahayoniyya.
Yana mai jaddada cewa: Iran ita ce ginshikin gwagwarmaya, don haka dole ne masu alakar da haramtacciyar kasar Isra’ila su yi tunanin yadda za su hada kai wajen yakar gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila.