Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannun kan dokar fara biyan N70,000 a matsayin albashi mafi karanci ga ma’aikata a Najeriya.
A ranar Litinin shugaban kasan ya rattaba hannu kan sabuwar dokar karin albashin a lokacin taron Majalisar Zartaswa ta Kasa (FEC), wanda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da sauran jagoroin bangaren majalisa suka halarta a Fadar Shugaban Kasa.
Halartarsu taron na da nasaba da zanga-zangar gama-gari da ke tafe a fadin Najeriya daga ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa.
Sanya hannun nasa bisa dokar na zuwa ne kwanaki biyu kafin fara zanga-zangar gama-gari kan tsadar rayuwa da yunwa a fadin kasar.
kafin sa hannun shugaban kasan, al’umma a Jihar Neja suka fara zanga-zanga kan halin da kasar ke ciki.
Matasan sun hau kan tituna suna daga kwaleye masu dauke da rubutu da ke nuna bacin ransu kan halin tsadar rayuwa a kasar.
Masu zanga-zangar sun rika rera wakokin nuna adawa da gwamnati a yayin da suke tattaki a kan tituna a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Gwamnonin tarayya da na jihohi suna yi yunkuri da dama na don dakatar da zanga-zangar, suna masu cewa zauna-gari-banza da makiya dimokuradiyya za su iya kwace ta.
A makon da ya gabata ne Gwamna Mohammed Bago na Jihar Neja ya ba wa al’ummar jihar da kayayyakin jin kai don hana zanga-zangar.