Tawagar dindindin ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta ce Amurka ta baiwa gwamnatin Isra’ila damar kai hare-hare ta sama kan Iran ta hanyar barin jiragen yakin Isra’ila su yi amfani da sararin samaniyar Iraki wajen harba makamai masu linzami a wuraren sojojin Iran da na radar.
Sanarwar ta kara da cewa, sararin samaniyar Iraki yana karkashin mamaya, da kuma iko na sojojin Amurka, wanda ta ce Amurka da hadin kanta ne aka aikata wannan laifin”.
A cikin wata sanarwa ta daban a jiya Asabar, ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama wadanda ta bayyana a matsayin keta dokokin kasa da kasa da kuma tsarin MDD, tana mai jaddada ‘yancin kasar na kare kanta daga hare-haren wuce gona da iri.
Ma’aikatar ta jaddada cewa wadannan ayyuka na nuni da yin barazana kai tsaye ga ‘yancin kan kasar Iran.
Sanarwar ta yi nuni da hakkin kare kai da Iran ke da shi, kamar yadda aka zayyana a shafi na 51 na Yarjejeniya Ta Duniya.
Iran ta ci gaba da cewa tana da hujja kuma wajibi ne ta kare kanta daga wuce gona da iri.
Gwamnatin Iran ta nanata kudurinta na amfani da duk wani abu da ake da shi don kare tsaronta.