Taron Masu Bada Tallafi Ya Bukaci A Gaggauta Kai Daukin Gaggawa A Fadin Gaza

Taron Jordan, kan yadda za’a taimakawa Gaza, ya bukaci da a gaggauta kai tallafin jin kai a fadin zirin. A sanarwar karshen taron, wadanda suka

Taron Jordan, kan yadda za’a taimakawa Gaza, ya bukaci da a gaggauta kai tallafin jin kai a fadin zirin.

A sanarwar karshen taron, wadanda suka shirya taron sun yi kira da a gaggauta kai dauki da agajin jin kai a duk fadin zirin Gaza.

A nasa bangare babban sakatare na MDD, ya ce “Dole ne a kawo karshen tashin hankalin.

Yakin da ake yi ya haifar da mummunan rikicin jin kai a yankin Falasdinu, inji Antonio Guteress a taron.

Ya kara da cewa kashe-kashen da ake yi a Gaza ya zarce duk wani abu da na fuskanta a tsawon shekarun da nake a matsayin sakatare-janar, na MDD” in ji shi.

Kasar Jordan dai ta gayyaci wakilai daga kasashe 75 da shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da dama zuwa taron, wanda Majalisar Dinkin Duniya, Jordan da Masar suka shirya tare.

“Babbar manufar taron ita ce cimma matsaya kan matakan da za a dauka don kula da bukatun da ake da su na yanzu-yanzu” a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments