A jiya Asabar ne dai da shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah yake cika kwanaki 40 da yin shahada, aka yi taron karawa juna sani na kasa da kasa anan birnin Tehran mai taken: “ Makarantar Nasarallah”
Taron wanda ya sami halartar manazarta daga cikin gida da kuma waje ya mayar da hankali akan yin bitar salon gwgawarmayar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah.
Daga cikin kasashen da su ka sami halarta da akwai Iraki,Bahrain, Masar, Kuwait, Turkiya, da India. Sai kuma Malazia, Aljeriya, da Tunisia.
Da yake gabatar da jawabi a wurin taron, shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran, Muhammad Bakir Qalibaf ya bayyana cewa; Shahid Sayyid Hassan Nasrallah ya tsorata abokan gaba a lokacin da yake a raye da kuma bayan shahadarsa.
Har ila yau shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran din ya kara da cewa; Shahid Sayyid Hassan Nasrallah ya riga ya kafa ka’idoji da dokokin gwgawarmaya, ya kuma kare batun Falasdinu a matsayin wani batu na musulunci.
Dangane da yakin da yake faruwa a kudancin Lebanon, shugaban majalisar ta Iran ya ce, tsayin dakar kungiyar ta Hizbullah ya sa har yanzu ‘yan sahayoniya ba su iya shiga ciki ba.
Shi kuwa mataimakin shugaban kasar Iran akan muhimman ayyuka Muhammad Jawad Zarif ya ce; Hizbullah tana nan a raye, haka nan kuma sauran kungiyoyin gwgawarmaya irin su Hamas da Jihadul-Islami.