Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Jiragen Ruwan Amurka A Tekun Bahar Maliya

Sojojin Yemen sun sanar da kai hare-hare kan jiragen ruwan Amurka guda uku a cikin tekun Bahar Maliya Kakakin Rundunar Sojin Yemen Birgediya Janar Yahya

Sojojin Yemen sun sanar da kai hare-hare kan jiragen ruwan Amurka guda uku a cikin tekun Bahar Maliya

Kakakin Rundunar Sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya sanar a yau Juma’a cewa: Dakarun kasar Yemen sun kai jerin hare-hare kan wasu jiragen yakin Amurka guda uku a tekun Bahar Maliya tare da nuna faifyai bindiyon.

Birgediya Janar Sari’e ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin ‘yan gwagwarmaya na “Imani da Jihadi da tsayin daka tare da Gaza da Lebanon” yana jaddada cewa: Dakarun kasar Yemen sun kai wasu jerin hare-haren soji masu inganci kan wasu manyan jiragen yakin Amurka guda uku a tekun Bahar Maliya yayin da suke kan hanyarsu ta tafiya haramtacciyar kasar Isra’ila domin ci gaba da gudanar da shirin tallafawa abokan gaba gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a yakin da take kaddamarwa kan al’ummar Falasdinu.

Ya kara da cewa, an gudanar da aikin hadin gwiwa tsakanin sojojin ruwa da na masu kula da makamai masu linzami da kuma sojojin sama masu kula da jiragen sama marasa matuka ciki gami da makamai masu linzami guda 23 ciki har da masu fuka-fukai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments