Sojojin Yemen Sun Fidda Hotunan Hare Haren Sa Suka Kai Kan Wani Jirgin ruwan kasuwanci na HKI Tare Da Amfani Da Makami Mai Linzami ‘Hypersonic”
Sojojin kasar Yemen sun fidda hotunan bidiyo na hare haren da suka kaiwa wani jirgin kasuwanci na HKI a tekun Arbian, wani lokaci a bayan.
Tashar talabijan ta Almasirah ta kungiyar Ansarallah ta yada hotunan wannan haren ne a ranar 26 ga watan Yunin da muke ciki. Labarin ya kara da cewa an yada wasu bayanai da suka fito tare da hotunan bidiyon, inda suka nuna cewa makami mai linzamin samfurin Hypersonic ne, wato yana sauri fiye da saurin sauti ninki –ninki, sannan sun bashi suna Hatem 2. Banda haka makamin yana da kayakin aiki na zamani wadanda suka hada iya sarrafashi daga nesa don samun bararsa ko da yana motsawa ko tafiya.
Har’ila yau makamin yana amfani da sandarerren makamashi sannan an samar da su a cikin tazara tazara daban daban.
Labarin ya kara da cewa jirgin ruwan kasuwancin HKI da sojojin suka kaiwa hare a tekun Arebian kuma shi ne MSC SARAH-V.
Daga karshen labarin ya ce kamfanonin kera makaman yaki na cikin gida ne suke kera makaman masu linzamin kamar sauran makaman da suke kerawa.
Tun bayan fara yakin tufanul aksa ne sojojin kasar Yemen suka shiga yaki da HKI inda take hana jiragenta na kasuwanci wuce da mashigar ruwa ta babul mandab, ko tekun red sea ko kuma kusa das u. Sannan ta kara da cewa ba zata daina yakin ba sai HKI ta dakatar day akin da take yi a gaza.