Sojojin Yahudawa Sun Yi Lugudan Wuta Kan Falasdinawa Da Ta Sanadin Shahada Da Jikkatansu

Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi luguden bama-bamai kan yankuna daban-daban na Zirin Gaza, inda aka samu shahidai da jikkata Falasdinawa masu yawa Falasdinawa

Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi luguden bama-bamai kan yankuna daban-daban na Zirin Gaza, inda aka samu shahidai da jikkata Falasdinawa masu yawa

Falasdinawa da dama sun yi shahada yayin da wasu suka jikkata daga daren jiya zuwa wayewar garin yau Juma’a, sakamakon luguden wuta da jiragen saman sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi kan yankuna daban-daban na Zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarto cewa: Wasu Falasdinawa 8 sun yi shahada a wani harin bam da sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suka kai kan wani gida na iyalan Abu Shakyan da ke Block C na sansanin Nuseirat da ke tsakiyar Zirin Gaza, ciki har da yara kanana.

Kamfanin dillancin labaran ya kara da cewa: Sannan wasu Falasdinawa 6 daga iyalan Abu Hassanein sun yi shahada sakamakon harin bam da jiragen saman sojin mamaya suka kai kan wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Bureij da ke tsakiyar Zirin Gaza.

Haka nan wasu Falasdinawa biyu kuma sun yi shahada a wani harin bam da jiragen saman mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a birnin Gaza, da kuma harba makamai masu linzami kan yankin kudancin unguwar Tal al-Hawa da ke kudu maso yammacin birnin na Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments