Sojojin Sudan Da Dakarun Kai Daukin Gaggawa Suna Ci Gaba Da Gwabza Fada A Jihar Sennar

Ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da Dakarun Kai Daukin Gaggawa a jihar Sennar ta kasar Sudan Kafofin watsa labaran Sudan

Ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da Dakarun Kai Daukin Gaggawa a jihar Sennar ta kasar Sudan

Kafofin watsa labaran Sudan sun yada labarin cewa: Jiragen saman yakin sojojin Sudan sun kai hare-hare kan wuraren tarurrukan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces a wasu kauyukan jihar Sennar dake kudu maso gabashin kasar, yayin da kungiyar ta Rapid Support Forces ta sanar da kashe daya daga cikin jagororinta a wani hari da sojojin kasar suka kai kan jihar ta Sennar.

Kafofin watsa labaran sun kara da cewa: Dakarun kai daukin gaggawan sun taru ne a kauyukan Al-Nuraniya, Al-Murif’a da Khor Al-Arab, da nufin tunkarar garin Mayerno da ke karkashin ikon sojojin Sudan. Jihar Sennar dai kusan a kullum rana tana ci gaba da fuskantar taho-mu-gama tsakanin sojoji da dakarun kai daukin gaggawa, musamman bayan da mayakan dakarun kai daukin gaggawa suka karbe iko da birnin Sinja, babban birnin jihar ta Sennar, inda dubban mazauna jihar suka tsere zuwa wasu jihohi irin Gedaref a gabas da Blue Nile a kudu.

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments