Sojojin Isra’ila Sun Bukaci “Dukkan Mutanen Arewacin Gaza” Su Fice Zuwa Kudanci

Sojojin Isra’ila sun jefa wasu takardu a kan birnin Gaza yau Laraba, suna kira ga “dukkan mutane” a arewacin yankin Falasdinu da aka yiwa kawanya

Sojojin Isra’ila sun jefa wasu takardu a kan birnin Gaza yau Laraba, suna kira ga “dukkan mutane” a arewacin yankin Falasdinu da aka yiwa kawanya da su fice zuwa kudanci ta hanyar amfani da “hanyoyi masu tsaro”, kamar yadda wani dan jarida na AFP, ya rawaito.

“Ga duk wadanda ke cikin birnin Gaza, hanyoyin masu tsaro suna ba ku damar yin tafiya cikin aminci daga birnin Gaza zuwa matsugunai a Deir el-Balah da Al Zawiya,” a cewar AFP.

“Birnin Gaza ya kasance yanki mai hatsarin gaske,” a cewar takardun gargadin da aka watsa kan Zirin na Gaza yau Laraba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran za a ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da kasar Qatar ke shiga tsakani yau Laraba, da nufin sako karin Isra’ilawan da Hamas ke garkuwa da su tun watan Oktoban bara.

Wakilan Amurka da na Isra’ila za su gana da manyan jami’an gwamnatin Qatar da kuma na Masar.

Fadar White House ta ce ana tattaunawar ne a cikin sirri da ake fatan ta kai ga cimma yarjejeniya mai inganci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments