Sojin Yeman Sun Kai Hare-hare Kan Jiragen Ruwa Da Ke Da Alaka Da Amurka Da Isra’ila A Gabar Tekun Kasar

Kakakin Rundunar Sojin Yaman ya ce sojojin ruwan kasar da na bangaren makamai masu linzami sun kai hare-hare uku kan jiragen ruwa da ke da

Kakakin Rundunar Sojin Yaman ya ce sojojin ruwan kasar da na bangaren makamai masu linzami sun kai hare-hare uku kan jiragen ruwa da ke da alaka da Amurka da Isra’ila a gabar tekun kasar, domin nuna goyan  Falasdinawa a ci gaba da farmakin da Isra’ila ke kaiwa Gaza.

Da yake magana a wani taron manema labarai da aka watsa kai tsaye daga Sana’a babban birnin kasar Yemen a daren jiya Talata, Birgediya Janar Yahya Saree ya ce sojojin kasar sun auka wa jirgin ruwan Amurka Maersk Sentosa da ke cikin tekun Arabiya da makamai masu linzami da dama.

Janar Sarea ya kara da cewa, sojojin ruwan kasar Yemen sun kai hari kan jirgin ruwan Marathopolis da ke gabar teku, da kuma jirgin MSC Patnaree da ke gabar tekun Aden da wasu jirage marasa matuka.

Ya jaddada cewa ayyukan guda uku sun cimma burinsu cikin nasara, daidai da yadda ake bukata.

Saree ya yi nuni da cewa, dakarun kasarsa za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yaki da Isra’ila har sai an tabbatar da tsagaita bude wuta a zirin Gaza, tare da dage duk wani takunkumin da aka sanya na kai kayan agaji ga mazauna yankin.

Ya kuma ce sojojin kasar Yemen sun shirya tsaf domin daukar mataki kan duk wani da zai goyi bayan Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments