Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin wanda yake ziyar aiki a kasar Korea ta Arewa ya bayyana cewa Karin yarjejeniya da suka cimma da kasar Korea ta Arewa a wannan ziyarar, taimakawa juna ne a duk lokacinda daya daga cikin kasashen biyu suka fata yaki da wasu kasashe.
Kamfanin dillancin labaran Tass na kasar rasha ya nakaltp shugaban Putin yana fadar haka jim kadan bayan rattaba hannu kan yarjeniyar tsaro da tokwaransa na kasar Koria ta Arewa Kim Jong Un a birnin Piyungyang.
Putin ya kara da cewa, a halin yanzu kasarsa tana yaki da wasu kasashen yamma yayann kungiyar tsaro ta NATO wanda suke tallafawa kasar Ukraine a fafatawan da take da kasar tun kimani shekaru biyu da suka gabata.
Shugaban kasar na Rasha ya kara da cewa, kasashen yamma musamman Amurka ba kasar Rasha da korea ta arewa kadai sukewa barazana ba. Kasashe da dama a yankin Asia suna fuskantar barazana daga wadannan kasashe. Kuma barazanar a fili yake saboda makamansu da suka jibge a wadan nan yankunan.