Shugaban kasar Iran Masa’ud Pezeskiyan yayi alkawarin bawa dukkanin mutanen kasar Iran damar samun arziki da ci gaba tare da adalci.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban Pezeshkian yana fadar haka jim kadan bayanda Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khamina’e ya mika masa shaidan tabbatar da shi a matsayin shugaban kasa na 9 tun bayan kafuwar JMI a shekara 1979.
Taron tabbatarwan dai ya sami halattar manya manyan baki na yan siyasa jami’an gwamnati da bangarorin tsaro daban daban.
Shugaban ya kara da cewa kasar Iran duk tare da yawan kabilunta tana da hadinkai saboda kiyaye dokokin kasa sannan tana da gwamnatin mai karfi wacce take iya tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Ya kuma sha alwashin tabbatar da cewa ya yi amfani da shawarorin jagoran juyin juya halin musulunci don tafiyar da kasar kamar yadda ya dace, da kuma samun hadin kan kasa.
Pezeskiyan ya kuma kammala da cewa ci gaban kasa ba zai samu ba sai da hadin kan mutanen kasar, don haka yana neman hadin kan mutanen kasar gabata daya don cimma wannan manufar.
Pezeshkian, dan shekara 69 a duniya ya zama shugaban kasar Iran ne a zaben shugaban kasa zagaye na 2 wanda aka gudanar a ranar 5 ga watan Yuli da muke ciki, tare da samun kuri’u 16,384,403