Shugaban Majalisar Shawara ta Musulunci ta Iran ya yi kira ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki matakin dakatar da laifuffukan da gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila ke yi kan Falasdinawa
Shugaban Majalisar Shawara ta Musulunci a Iran Muhammad Baqir Qalibaf, ya yi kira ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki matakin gaggawa na dakatar da laifukan da yahudawan sahayoniyya suke yi a Gaza.
Ghalibaf ya jaddada a cikin wata wasika da ya aike wa shugabannin majalisun kasashen duniya a jiya Talata cewa: Ya zama wajibi kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya dauki kwararan matakai da gaggawa don dakile laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aiwatarwa a Zirin Gaza da cikakken goyon bayan Amurka da wasu kasashen yammacin duniya.
Ya zo cikin wasikar cewa: Tsawon watanni 10 da bullar rikicin Gaza da ci gaba da aikata manyan laifuka ta hanyar kai hare-haren wuce gona da iri da gangan kan al’ummar Falastinu da ba su ji ba ba su gani ba, na nuni da rashin amfani da siyasa a bangaren gwamnatin ‘yan sahayoniyya don haka akwai bukatar mayar da ita saniyar ware domin tilasta mata kawo karshen wannan kazamin yaki da ke ci gaba da janyo bala’in jin kai a Gaza.