Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan ya fitar da kudurin dakatar da ayyukan ministocinkasar guda 3
Shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin kasar Sudan kumababban hafsan hafsoshin sojin kasar Abdel Fattah Al-Burhan, ya fitar da wata matsaya ta dakatar da ayyukan ministocin harkokin wajen kasar Hussein Awad, da na yada labarai Graham Abdelqadir, da ministan kula da walwala, Osama Ahmed, tare da nada wadanda za su maye gurbinsu.
Majalisar Gudanar da Mulkin Sudan ta ce, a cikin wata sanarwa da ta fitar, Al-Burhan ta fitar da wani kuduri na amincewa da matakin da majalisar ministocin gwamnatin rikon kwaryar kasar ta dauka, na dakatar da aikin Hussein Awad Ali Muhammad daga kan mukamin ministan harkokin wajen kasar, tare da amincewa da nadin na majalisar ministocin kasar Ali Youssef Al-Sharif a matsayin sabon Ministan Harkokin Waje.
A ranar 17 ga watan Afrilu ne Al-Burhan ya nada Hussein Awad a matsayin ministan harkokin wajen kasar, sannan ya sallami Ali Al-Sadiq daga kan mukamin na ministan harkokin wajen kasar.
Sannan a ranar Lahadi ne, Al-Burhan ya fitar da matakin dakatar da ministan al’adu da yada labarai, Graham Abdul Qader daga aikinsa, da kuma amincewa da nadin Khaled Ali Al-Aysar.