Shugaban Kungiyar Ansarullah Ta Yemen Ya Ce; Dole Ne Faladinawa Su Kai Harin Guguwar Al-Aqsa

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Harin guguwar Al-Aqsa ya kasance dole don neman hana dukkanin zalunci da laifukan haramtacciyar kasar Isra’ila

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Harin guguwar Al-Aqsa ya kasance dole don neman hana dukkanin zalunci da laifukan haramtacciyar kasar Isra’ila

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdul Malik Badruddeen al-Houthi, ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya sun hada dukkan karfinsu, kuma a bayansu akwai Amurka da Birtaniya da kuma kasashen Yamma da suke goyon bayan kai farmaki kan Gaza, yana mai jaddada cewa: Makiya haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi amfani da kowace hanya wajen aiwatar kisa da kisan kiyashi da kashe-kashe ta hanyar amfani da yunwa kan Falasdinawa, yana mai jaddada cewa: Harin guguwar Al-Aqsa wani lamari ne da ya wajaba a kaddamar da shi wajen kalubalantar dukkan wuce gona da iri na haramtacciyar kasar Isra’ila.

A cikin jawabin da ya yi kai tsaye gaal’ummar Yemen, Sayyid Al-Houthi ya tabbatar da cewa: A tsawon shekara guda, makiya yahudawan sahayoniyya sun kaddamar da hare-hare sama da suka kai sau rubu’in miliyan guda da kuma luguden wuta ta hanyar jiragen yaki kan Zirin Gaza.

Yana mai nuni da cewa: Akwai kimanin shahidai 150,000, da wadanda suka bace da kuma jikkata a Zirin Gaza, inda ya kara da cewa; Makiya yahudawan sahayoniyya sun yi amfani da bama-bamai kimanin tan dubu 100 da suka hada da bama-bamai da makamai masu linzami da makamai masu guba da Amurka ta gabatar musu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments