Shugaban kasar Turkiyya ya bayyana cewa; Kasarsa ta yanke huldar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila
Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya jaddada cewa: Kasarsa ta yanke huldar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma tana ci gaba da kasancewa tare da Falasdinu har zuwa karshe.
Wannan dai ya zo ne a cikin sanarwarsa ga manema labarai bayan dawowa daga ziyarar da ya kai kasar Saudiyya domin halartar babban taron hadin gwiwa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, da kuma kasar Azarbaijan domin halartar taron kasashen da ke cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya. (COP29).
Erdogan ya jaddada cewa: Hadin kai a tsakanin al’umma musamman jam’iyyar mai Mulki a Turkiyya ta jam’iyyar Adalci da ci gaba da jam’iyyar kishin kasa sun tsaya tsayin daka wajen yanke hulda da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, wanda hakan ke nuni da cewa: Turkiyya za ta ci gaba da yin hakan a mataki na gaba.
Dangane da haka, Erdugan ya ce: Sun yanke huldar kasuwanci da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma suna goyon bayan al’ummar Falasdinu har zuwa karshe.
Shugaba Erdugan ya kara da cewa: Turkiyya ce kasar da ta nuna mafi girman martani a duniya kan rashin adalcin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma ta dauki matakai masu muhimanci da suka hada da dakatar da huldar kasuwanci da ita.