Shugaban mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ya taya Masoud Pezeshkian murnar zabensa da aka yi a matsayin sabon shugaban kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Shugaban majalisar rikon kwarya a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahman Tiani, ya aike da sakon taya murna ga zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, tare da jaddada yin kira da a samu karfafan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
A sakon da shugaban majalisar rikon kwarya ta Jamhuriyar Nijar ya aikewa zababben shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Tsabtataccen zaben da aka yi na shugaban kasa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya Sanya shi farin ciki tare da zaburar da shi kan bayyana murnarsa da na Majalisar dukkanin al’ummar Nijar jami’anta da al’ummarta.
Ya kara da jaddada fatan samun cikakkiyar nasara wajen gudanar da wannan muhimmin aiki da ya rataya a wuyar sabon shugaban kasar ta Iran Masoud Pezeshkian.