Shugaban Kasar Mauritaniya Ya Sake Samun Nasarar Zaben Shugabancin Kasar Karo Na Biyu

Shugaban kasar Mauritaniya ya samu gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasa karo na biyu a kasar Mauritaniya Hukumar zabe a Mauritaniya ta sanar da nasarar

Shugaban kasar Mauritaniya ya samu gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasa karo na biyu a kasar Mauritaniya

Hukumar zabe a Mauritaniya ta sanar da nasarar shugaba Mohamed Wuld Ghazouani mai barin gado a wa’adi na biyu na shugabancin kasar bayan samun kuri’u sama da kashi 65 cikin dari na kuri’un masu zabe, yayin da dan takara Biram Al-Dah Ould Abeid ya zo na biyu.

A daidai lokacin da aka fara kidaya sakamakon farko na zaben shugaban kasa da aka gudanar a birnin Mauritaniya, fadar mulki kasar Nouakchott, da alama an samu kwanciyar hankali, sai dai duk da haka an tsauraran matakan tsaro domin ganin akwai yiwuwar bullar tarzoma, wanda dan takara Biram Ould Al-Dah ya nuna alamun hakan, yayin da ya sanar da kin amincewa da sakamakon zaben, kamar yadda ya yi kira ga jama’a da su fito kan tituna don gudanar da zanga-zanga har sai an samu ingantaccen tsari dimokradiyya, kamar yadda ya ce.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Mauritaniya ya fitar da sanarwa da a ciki ya tabbatar da cewa: Mohamed Ould Sheikh Ghazouani ya sake lashe zabe a karo na biyu a karon farko na zaben kasar, sabanin sanarwar dan takara Biram ya fitar cewa ya yi imanin za su iya janyo sake gudanar da zabe zagaye na biyu a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments