A yau Alhamis ne Korea Ta Arewa ta sanar da cewa shugaban kasar Kim Jung Un ya sa ido akan gwajin da kasar ta yi na makami mai linzami mai cin dogon zango saboda kara Karfin kasar ta fuskar kariya da makaman Nukiliya.
Da yake jawabi a wurin gwajin, shugaban kasar ta Korea Ta Arewa ya bayyana cewa: Wannan gwaji ne a fagen aikin soja, wanda manufarsa ita ce isar da sako ga abokan gaba akan azamarmu ta mayar da martani.”
Kwanaki biyu da su ka gabata ne dai kasar Korea Ta Kudu ta yi gargadin cewa, makwanciyarta ta Arewa tana shirin yin gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango, watakila kuma har da gwajin makamin Nukiliya.