Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan zai yi tafiyarsa ta farko zuwa kasat Iraki wanda kuma shine tafiyarsa ta farko zuwa kasashen waje tun bayan ya zama shugaban kasa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa shugaban zai je kasar ta Irakin ne bisa gayyatar tokwaransa na kasar Abdul-Lateef Rashid.
Kafin haka dai kasashen biyu suna da tsohuwar dangantaka mai karfi a tsakaninsu, kuma a baya bayan nan kadaddashin ministan harkokin wajen na lokacin Ali Bakiri Kani ya je kasar ta Iraki don rage matsalolin da suka tashi a tsakanin kasashen biyu.
Banda haka kasashen biyu suna da yarjeniyoyi da dama wadanda suka shafi, tattalin arziki siyasa tsaro da sauransu.
A gwamnatinn marigayi shugaba Ra’isi dai kasashen biyu sun cimma yarjeniyar kammala aikin layin dogo wanda zai hada kasashen biyu daga kudancin kasashen nasu.
Banda haka ana saran tafiya ta biyu zuwa kasashen wajen na sabon shugaban shi ne halattar taron babban zauren MDD a birnin New York na kasar Amurka a cikin watan Satumba mai zuwa.