A yau larabace ake makokin shahadar limami na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) wato Imam Aliyu bin Musa(a) wanda akewa lakabi da Reza.
Imam Reza, yayi shahada ne a shekara ta 203 a hannun sarki Mamun daya daga cikin sarakunan abbasiyawa na lokacin, wato Sarki Mamun dan Sarki Haruna Rasheed. Wanda kuma yake da mazaunin mulkinsa a birnin Maru na yankin Khurasan.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa shugaba Ma’ud Pezeskiyan ya sami tarbar shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhamad Bakir Kolibof, tare da tawagarsa, sannan ya shiga cikin masu makokin shahadar limami na 8 daga yayan manzon All..(s).
A rana irin ta yau ce 31 ga watan Safar shekara ta 203 HK, sarki Mamun ya kashe Imam Riza (a) da guba bayan ya kasa raba shi da masoya iyalan gidan manzon All..(s) a yankin Khurasan da sauran wurare. Kuma a bana, masoya da kuma masu kaunar iyalan gidan manzon All..(s) kimani miliyon 5 ne suka sami damar ziyartar limamin a ranar shahadarsa.
Labarin ya kammala da cewa shugaban kasar ya zabi fara tafiyarsa zuwa Mashad a matsayin tafiya ta farko zuwa wata jiha a kasar tun lokacinda ya zama shugaban kasa.