Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Cewa: Falasdinu Ta Zame Batun Da Ta Mamaye Duniya A Halin Yanzu

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Falastinu a yau ita ce batu na farko kuma gama gari ga dukkan kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Sayyid

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Falastinu a yau ita ce batu na farko kuma gama gari ga dukkan kasashen musulmi

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da tawagar manyan marubuta da masana adabi da al’adu na kasashen musulmi da suka halarci taron baje kolin littattafai na kasa da kasa karo 35 na birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai fayyace cewa: Makiya a yau suna kokarin jagorantar ra’ayoyin al’ummar kasashen duniya game da batun Gaza, sun mamaye kafofin yada loabarai, inda suke watsa labaran karya da gurbata hakikanin gaskiya, tare da jaddada mahimmancin matsayi da alhakin da ya doru kan masu alƙaluma da al’ada wajen magance wannan makirci.

Shugaban kasar ya kuma jaddada cewa: Makiya a yau suna kokarin jagorantar ra’ayoyin al’umma kan lamarin Gaza, kuma lamarin Falastinu ya zama batu na farko kuma na gama gari tsakanin dukkanin al’ummar musulmi da ‘yantattun kasashe, kuma hadin kai da batun Falasdinu ya haifar ana daukarsa a matsayin tushen nasarar karshe ta al’ummar Falastinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments