Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Bukatar Karfafa Alakar Tattalin Arziki Da Kasar Afirka Ta Kudu

Zababben shugaban kasar Iran ya jaddada bukatar karfafa alakar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka ta Kudu A yayin ganawarsa da ministan hulda da kasa

Zababben shugaban kasar Iran ya jaddada bukatar karfafa alakar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka ta Kudu

A yayin ganawarsa da ministan hulda da kasa da kasa da hadin gwiwa na kasar Afirka ta Kudu Ronald Usi Lamela, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada bukatar bunkasa huldar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka ta Kudu.

Pezeshkian ya jaddada muhimmancin karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen Iran da Afirka ta Kudu a fannonin da suka shafi kasashen biyu, gami da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa, ciki har da tsarin kungiyar BRICS, yana mai cewa: Bisa la’akari da mabanbantan damar da ake da su, yana fatan kara karfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu tare da kara bunkasa su.

Har ila yau, shugaban kasar na Iran ya bayyana jin dadinsa ga matsayin sada zumunci na siyasa na kasar Afirka ta Kudu, musamman matakan da gwamnatin kasar ta dauka da nufin saukakawa da kuma gaggauta shigar da Iran cikin kungiyar BRICS.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments