Shugaban Iran Ya Ce: Taimakawa ‘Yan Gwagwarmaya Yana Daga Cikin Muhimman Manufofin Kasarsa

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da taimakawa ‘yan gwagwarmaya na daya daga cikin muhimman manufofin kasarsa Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da taimakawa ‘yan gwagwarmaya na daya daga cikin muhimman manufofin kasarsa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi la’akari da kokarin karfafa alaka da kasashen musulmi da samar da hadin kai a tsakanin al’ummomin musulmi a cikin muhimman manufofin gwamnatin Iran na harkokin waje tare da jaddada wajabcin hadin kan al’ummar musulmi wajen tunkarar zaluncin yahudawan sahyoniya da kuma dakatar da laifukan gwamnatin yahudawan da take aikatawa a Gaza.

A ganawar da ya yi da mataimakin babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassim, wanda ke ziyara a birnin Tehran domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasar Iran, Pezeshkian ya yaba da tsayin daka da kuma jajurcewar da ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullah suke yi a fagen kalubalantar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yan mamaya, sannan ya jaddada goyon baya da taimakon kungiyar gwagwarmaya a matsayin wani wajabci na addini kuma daya daga cikin manufofin siyasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Shugaban na Iran ya kuma bayyana munanan laifukan da yahudawan sahayoniya suka aikata a kan al’ummar Gaza da ake zalunta, da kuma goyon baya da Amurka da wasu kasashen yammacin duniya suke baiwa wadanda suke aikata muggan laifuka kan dan Adam.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments