Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Duniya Ya Iso Iran

A jiya Laraba da marece ne dai shugaban hukumar Makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya iso Tehran domin tattaunawa da mahukuntan kasar.

A jiya Laraba da marece ne dai shugaban hukumar Makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya iso Tehran domin tattaunawa da mahukuntan kasar.

Daga cikin wadanda su ka tarbi Grossi a filin saukar jiragen sama na  “ Mehrabad” da akwai shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasar Iran Behruz Kamalondi, da kuma kakakin hukumar.

Gabanin isowar  Grossi Tehran, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa;  Aiki a tsakanin Iran da hukumar ta kasa da kasa yana tafiya daidai.

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce, saboda sabon ruhin da ake da shi na alaka a tsakanin bangarorin biyu,yanzu an samar da yanayin da za a hau sabuwar turba.

A yayin wannan ziyarar tashi, Rafael Grossi zai yi tattaunawa da  shugaban hukumar makamashin Nukiliya na Iran da kuma wasu manyan jami’an gwamnatin Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments