A ganawarsa da shugaban kasar Estonia, Sheikh Al-Azhar ya yi Allah wadai da laifukan yaki na yahudawan sahyoniyawa a Gaza tare da bayyana wadannan laifukan da ba za a iya misalta su ba.
A rahoton jaridar Al-Yum Al-Sabi, Sheikh Ahmed Al-Tayeb, Sheikh Al- Azhar ya gana da shugaban kasar Estoniya Alar Karis, inda suka tattauna kan hanyoyin karfafa hadin gwiwa.
A cikin bayaninsa ya ce: Sakon Musulunci shi ne yaduwar zaman lafiya a duniya, kuma wannan shi ne sakon da Azhar ta ginu a kansa sama da shekaru dubu.
Al-Azhar tana koyar da ilimin addini da harshe tare da karbar bakuncin dalibai musulmi daga dukkan kasashen duniya domin su yada abubuwan da suka koya na dabi’u, adabi, zaman lafiya da ‘yan uwantaka a kasarsu.
Da yake ishara da cewa sama da dalibai 60,000 daga kasashe sama da 100 ne wannan cibiya ke koyar da su, Sheikh Al-Azhar ya bayyana cewa, Azhar a shirye take ta ba da tallafin karatu ga Musulman Estoniya domin su samu damar karatu a jami’ar Azhar.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da kisan gillar da ake yi wa al’ummar Gaza, Sheikh Ahmed Al-Tayeb ya bayyana laifukan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da cewa abu ne da ba ya misaltuwa, ya kuma jaddada cewa: zukatanmu sun cika da bakin ciki na kisan gillar da ake yi wa kananan yara da mata da matasa da kuma tsofaffi. Ba su yi wani zunubi ba face sun dage da zama a cikin kasarsu tare da shan alwashin ba za su bar ta ba.
Yayin da yake yaba matsayin Estoniya na yin Allah wadai da zaluncin gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila a Gaza, da kuma kyakyawar matsayar kasar na amincewa da Palastinu a matsayin cikakkakiyar mamba a zauren Majalisar Dinkin Duniya, ya jaddada cewa, wannan matsayi na nuni da yadda Estoniya ta himmatu wajen tabbatar da ka’idojin jin kai da adalci da dokoki na kasa da kasa, da kuma kara goyon bayan gamayyar kasa da kasa kan hakkin falastinawa Falasdinawa.