Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lbanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa gwamnatin HKI tana cikin kwanaki mafi muni a rayuwar kasar na tsawon shekaru 76 da suka gabata saboda yakin tufanul Aksa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Nasarallah yana fadar haka a jawabin da ya gabatar na ranar Ashoora wato 10 ga watan Muharram na wannan shekarar a dandanin Imam Hussain (a) dake birnin Birut babban birnin kasar ta Lebanon.
Shugaban kungiyar ya kara da cewa idan gwamnatin HKI ta kuskura ta farwa kasar Lebanon da yaki to kuwa za ta ga abin mamaki, don buta wata tankar yakinta da zai rage.
Tun farkon watan octoban shekarar da ta gabata ce dakarun kungiyar suke fafatawa da sojojin HKI, bayan fara yakin Tufanul Aksa a Gaza, amma musayar wutan ya takaita a kudancin kasar Lebanon da kuma arwacin kasar Falasdinu da aka mamaye ne. HKI ta kasa shiga yaki gadan gadan da kungiyar a Lebanon.
Nasurallah ya jaddada cewa kungiyarsa zata ci gaba da tallafawa Falasdinawa wadanda suke fatatawa da sojojin HKI tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata a Gaza, har zuwa lokacinda zasu dakatar da yakin.
Ya zuwa yanzu dai sojojin HKI sun kai falasdinawa kimani dubu 39, ga shahada a yayinda wasu dubban suka ji rauni. A halin yanzu kimani watanni 10 ke nan da fara yakin amma sojojin yahudawan duk tare makaman da suke samu daga Amurka da kuma kasashen yamma sun kasa cimma manufarsu ta kwato yahudawan da suke tsare a Gaza ko kuma shafe kungiyar Hamas. Banda kungiyar Hizbullah dai, sojojin kasar Yemen da dakaru masu yaki da yan ta’adda a Iraki duk suna taimkawa Falasdinawa a yakin da suke fafatawa a Gaza.