Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ya jaddada cewa: Ga masu kokarin tsoratar da su da kisa, su sani su mutane ne da ba sa tsoron yaki
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hasan Nasrallah ya jaddada cewa: Halartar zaman juyayin Ashura wata shaida ce da take nuni da yadda al’umma suke da alaka da wannan al’ada, yana mai nuni da cewa a dukkan wuraren da ake gudanar da taron tunawa da ranar Ashura tare da dimbin jama’a, babu wani abin da ya faru na tsaro, sai dai wani abin takaici da ya faru a masarautar Oman, inda aka kashe wasu fararen hula da ‘yan sanda, don haka suna jajantawa shahidan.
A jawabin da Sayyid Nasrallah ya gabatar a wajen taron juyayin Ashura a dare na goma na watan Muharram da kungiyar Hizbullah ta shirya a filin Ashura da ke unguwar Al-Jamous da ke kudancin birnin Beirut, Sayyid Nasrallah ya gode wa ‘yan’uwa da suka halarci wannan zaman juyayi da dukkan sauran al’umma, iyalai masu daraja da suka halarci dukkan zaman juyayin.
Ya bayyana cewa, bisa kididdigar da suka yi, adadin wadanda suka halarci zaman juyayin Ashura a bana ya zarce na bara, duk kuwa da yanayin tsaro. Sannan ya kuma gode wa sojoji da jami’an tsaro na Lebanon bisa kokarin da suka yi wajen tabbatar da zaman lafiya a lokutan juyayin Ashuran. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: “Musulmi gaba daya ba tare da la’akari da mazhabarsu ba, suna son Ahlul-Baiti wato iyalan gidan Manzon Allah (amincin Allah ya tabbata a gare su), kuma wannan lamari ne na kowa-da-kowa,” ya kuma jaddada cewa, barazanar tsaro da wasu masu tsaurin ra’ayi da jahilci suka yi. bai hana gudanar da juyayin Ashura ci gaba ba.