Sayyid Husi:  Tsakanin Biden Da Trump Ba Wanda Ya Isa Hana Mu Taimakon Gaza

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen wanda ya gabatar da jawabi a jiya Alhamis, ya bayyana cewa;  Trump bai isa hana su cigaba da taimaka

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen wanda ya gabatar da jawabi a jiya Alhamis, ya bayyana cewa;  Trump bai isa hana su cigaba da taimaka wa Gaza ba, kamar yadda Biden bai isa ba. Haka nan kuma ya ce; Ba kuma shugabannin na Amurka kadai ba, babu wani mai laifi da zai kawar da Yemen daga kan tafarkin da take kansa na taimaka wa ‘yan gwgawarmaya.

Jagoran na kungiyar Ansarullah ya kuma yi kira yi al’ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwwatarsu a yau Juma’a domin gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya ga gwgawarmaya.

Sayyid Abdulmalik al-Husi, ya kuma yi ishara da laifukan yakin da HKI take tafkawa a Gaza, na yi wa Falasdinawa kisan kare dangi da rusa duk wani abu da rayuwa take da bukatuwa da shi a wannan yankin.

Bugu da kari jagoran na  kungiyar Ansarullah ya yi bayani akan yadda HKI ta hana shigar da kayan abinci cikin yankin Gaza,haka nan magani, tare da tilastawa mutane yin hijirar dole Arewacin Gaza.

Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma bayyana cewa, saboda ‘yan mamaya sun ci kasa a fagen daga, sun koma amfani da siyasar jefa mutanen Gaza cikin yunwa domin durkusar da su,su mika wuya, sai dai a nan ma sun gajiya.

Jagoran na Ansarullah ya kuma yi bayanin yadda duniya ta yi shiru tana kallon yadda ‘yan mamaya suke cigaba da aikata laifuka a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments