Sayyid Husi: Hizbullah Tana Da Karfi Fiye Da Baya

Shugaban kungiyar Ansarullah,sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon tana da karfi a wannan lokacin fiye da zamanin baya. Sayyid Abdulmalik

Shugaban kungiyar Ansarullah,sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon tana da karfi a wannan lokacin fiye da zamanin baya.

Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Da Lebanon da Falasdinu suna fuskantar abokin gaba ne guda daya, tare da yin ishara da laifukan yaki da HKI take tafkawa a Gaza wand aba shi da tamka, sai dai kuma duk da haka ba su cimma manufarsu ba.

Shugaban Ansarullah ya kuma ce; Manufar shelanta yakin da HKI ta yi akan Lebanon shi ne hana Hizbullah cigaba da taimakawa Falasdinawa.

Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana gamsuwarsa da cewa; Abokan gaba, Isra’ila za su ci kasa matukar su ka yi gigin shiga cikin Lebanon da sojojin kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments