A sanarwar bayan taronsu na koli da suka gudanar a wannan Laraba, a birnin Kazan na kasar Rasha, kasashen BRICS sun bayyana damuwarsu game da karuwar tashe-tashen hankula a yankin yammacin Asiya tare da yin Allah wadai da matakin da gwamnatin Isra’ila ke dauka.
Kasashe mambobin na BRICS a cikin bayanin karshe na taron nasu, sun bayyana matukar damuwarsu game da rikice rikicen dake faruwa da rashin zaman lafiya a yankin yammacin Asiya.
Shugabannin kasashen BRICS sun yi Allah wadai da harin da gwamnatin Isra’ila ta kai kan ofishin jakadancin Iran a kasar Siriya, sun kuma yi Allah wadai da hare haren na’urorin sadarwa a kasar Lebanon.
Kasashen BRICS sun kuma yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya a kasar Labanon da kuma barazanar da ake fuskanta a harkokin tsaronsu, inda suka bukaci gwamnatin Isra’ila da ta gaggauta dakatar da hakan.
Kasashen sun Jaddada mahimmancin aiwatar da Tsarin Haɗin gwiwa na Aiki (JCPOA)
Muna jaddada muhimmancin aiwatar da cikakken aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran a karkashin kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 kuma muna jaddada mahimmancin tsarin da ya dace bisa fatan dukkan masu ruwa da tsaki don sake dawo da cikakken aiwatar da wajibcin JCPOA ta kowane bangare.
A wani bangare kuma Bisa bayanin karshe na taron kolinsu kasahen na BRICS sun sake jaddada goyon bayansu na baiwa Falasdinu matsayi na cikakiyar mamba a MDD.
Shugabannin BRICS sun kuma yi kira da a karfafa tsarin hana yaduwa da kwance damara domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya, tare da gaggauta aiwatar da kudurorin “kafa yankin da ba shi da makaman nukiliya da sauran makaman kare dangi a Gabas ta Tsakiya”.
Sun Yi kira da a kara kaimi ga kasashen da ba su ci gaba ba, musamman na Afirka, da Latin Amurka, da Caribbean, a cikin matakai da tsarin yanke shawara na duniya da daidaita su.
Shugabannin BRICS kuma suna son daukar karin matakai managarta a Afghanistan don hana ‘yan ta’adda amfani da yankunan kasar.
Muna jaddada bukatar samar da mafita cikin sauri da kwanciyar hankali a Afghanistan domin karfafa tsaro da zaman lafiyar yankin.
Kasashen BRICS na son ci gaba da ba da goyon bayan shawarwari da zaman lafiya a kasar Yemen karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya.
Kasashen BRICS sun kuma yi kira da a sake nazari kan ababen more rayuwa na kasa da kasa domin tunkarar matsalolin kudi da duniya ke fuskanta a yau.
Muna jaddada bukatar sake fasalin tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa a halin yanzu don fuskantar kalubalen hada-hadar kudi na duniya, gami da gudanar da harkokin tattalin arziki na duniya, don sanya tsarin tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa ya zama cikakke da adalci.
Shugabannin kasashen BRICS sun yi alkawarin daukar kwararan matakai na dakile yaduwar akidar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi.
Mun himmatu wajen daukar kwararan matakai na hanawa da dakile yaduwar akidar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, da yin amfani da fasahohin zamani da ake amfani da su wajen ayyukan ta’addanci, zirga-zirgar ‘yan ta’adda ta kan iyaka, ba da tallafin kudi na ta’addanci, da sauran nau’o’in tallafawa ta’addanci. .
A cikin sanarwar bayan taron nasu karo na 16 kassashen na BRICS, sun jaddada bukatar yin shawarwari da shiga tsakani don warware rikicin Ukraine ta hanyar tattaunawa cikin lumana, sun kuma bayyana damuwarsu game da karuwar tashe-tashen hankula da karuwar matsalar jin kai a Sudan tare da yin kira da a tsagaita wuta.
A ranar Laraba ne shugabanin kasashe mambobin BRICS, suka halarci taron kolin kungiyar karo na 16 a binrin Kazan.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian na daga cikin shugabannin mahalrta taron
Baya ga Pezeshkian, shugabannin kasashen Rasha, China, Afirka ta Kudu, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Fira Ministan Indiya za su halarci taron.
A wannan Alhamis, shugaban kasar Iran zai halarci taron kasashen BRICS Plus, wanda ya hada da kasashe masu sha’awar yin hadin gwiwa da kawancen BRICS, karkashin tutar “BRICS da Global South.”
Mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin siyasa na fadar shugaban kasar ya bayyana cewa, shugaba Pezeshkian zai gabatar da jawabai uku a taruka daban-daban na BRICS, tare da yin shawarwari tsakanin shugabannin kasashen Rasha, Sin, Indiya, Masar, da sauran kasashen duniya, domin kulla alaka.
An bayyana cewa tawagogi daga kasashe 36 zasu halarci taron kungiyar kasashen ta BRICS da arzikinsu ke bunkasa.
Akwai yiwuwar kasashen su kulla yarjejeniya kan sabon tsarin hada-hadar kudi tsakaninsu wadanda babu ruwansu da dalar Amurka.