Sakon godiyar Imam Khamenei ga tawagar Iran a gasar Olympics ta Paris

Imam Khamenei ya mika godiyarsa ga ‘yan wasan kasar Iran da shuwagabannin kungiyoyi da masu horar da ‘yan wasa a cikin sakon da ya aike

Imam Khamenei ya mika godiyarsa ga ‘yan wasan kasar Iran da shuwagabannin kungiyoyi da masu horar da ‘yan wasa a cikin sakon da ya aike ga tawagar Iran da ta halarci gasar Olympics ta 2024.

Bayan wasikar da shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa ya aikewa jagoran juyin juya halin Musulunci da gabatar da rahoto kan nasarorin wasanni da mambobin ayarin wasanni na Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka samu a gasar wasannin Olympics, Imam Khamene’i ya nuna matukar godiyarsa ga ‘yan wasan da kyakkyawar niyyarsu, wanda kuma Imam Khamenei ya rubuta hakan ne a amsar da ya bayar ga wasikar shugaban kwamitin Olympics na kasa.

Shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Iran Mahmud Khosraviwafa a cikin wasikar da ya rubuta dangane da nasarorin da ayarin wasanni na Jamhuriyar Musulunci ta Iran mai taken “Khadem al-Reza ” ya ambato wasu nasarorin wasanni na ‘yan kasar. Ya ce, ‘yan wasa ciki har da mata, sun nuna bajintar da hazaka da b a taba ganin irinta ba a cikin ayarin wasannin motsa jiki na Iran da kuma irin hazakar da matan suka nuna, da kuma lashe muhimman kambuna a wasu fannonin wasanni a karon farko a wasannin Olympics.

A gasar Olympics da aka yi a birnin Paris na wannan ta shekara ta 2024, tawagar Iran sun samu lambobin yabo a fannoni da dama, inda suka zama zakaru a wasan kokawa daTaekwondo  a tsakanin kasashe sama da 200 da suka halarci gasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments