Iran: Sabon maganinmu na cutar kansa na da inganci matuka

Pars Today- Wani kamfani na Iran ya samar da sabbin magungunan da aka yi domin masu fama da cutar kansa. Ali Aqajani, daraktan bunkasa harkokin

Pars Today- Wani kamfani na Iran ya samar da sabbin magungunan da aka yi domin masu fama da cutar kansa.

Ali Aqajani, daraktan bunkasa harkokin kasuwanci na kamfanin ya ce, “A bana mun samu damar samun sabbin magungunan rigakafin cutar da ke hannun wani kamfani na Biritaniya.”

A cewar Pars Today, wannan kamfani ya sami nasarar samar da magungunan rigakafin cutar kansa tare da fasahar Antibody-ADCs).

Aqajani ya kara da cewa, “Wannan maganin ana kiransa Tederox kuma ana amfani da shi wajen magance cutar kansar nono da wasu cututtuka masu alaka da tsarin narkar da abinci.

Yana iya karawa masu ciwon daji rai da yawa, kuma saboda maganin da aka yi ana allurar da su a jiki ta yadda ba za mu samu matsala ta rasa abubuwa da kan faru sanadiyyar kamuwa da cutar daji ba.

Abubuwan da suke faruwa sakamakon kamuwa da ciwon daji kamar zubewar gashi ko asarar nauyi; kuma a karshe, za mu shaida tasiri mafi girma.”

Da yake ishara da sabon maganin da ya yi fice wajen rigakafin kamuwa da cutar kansa, ya ce, “A halin yanzu, muna cikin tsarin samar da magunguna da yawa kuma farashin bai kai kashi 10 cikin 100 na irin na kasashen waje ba, samfurin maganin na kasashen waje $3000 ne kuma muna bayar da shi akan $200.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments