Kwanaki kadan gabanin tsagita wuta a Lebanon, ron Dermer yana kai da komowa a tsakanin Moscow da Tel Aviv da Washington.
A wancan lokacin, babu wanda ya san dalilin waccan zirga-zirgar tashi, amma a zahiri ana fassara ta da cewa tana da alaka Leba non. Shi kuwa Ron Dermer ya kasance ministan muhimman abubuwa na gwamnatin Netanyahu. Dabi’ar aikinsa kuwa ba ta takaita a cikin yadda za a shata makomar fage daya na yaki ba,abinda ya rika yi shi ne yadda zai samowar shugaban gwamnatinsa Netanyahu mafita a cikin laifukan da yake tafkawa a cikin wannan yankin. Ya kuma ba ta sigar da maigidan nashi da Isra’ila za su ci moriyarta a siyasance da kuma fagen yaki. Yana kuma son yin hakan ne a tare da samar da fahimtar juna a matsakin manyan masu taka rawa a cikin yakin Ukiraniya da kuma gabas ta tsakiya.
A karshe, an kai ga cimma tsagaita wutar yaki a Lebanon, sai dai kuma adaidai wancan lokacin an cimma wasu manufofin biyu masu kama da juna ta hanyar Moscow da Washington.
Me ya faru?
Bayan da Biden na Amurka ya bai wa Ukiraniya izinin ta yi amfani da makamai masu linzami dake cin nisan zango, na Amurkan da wadanda kasashen turai su ka bata, akan Rasha, zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fahimci cewa ana son yi wi alkawalinsa na kawo karshen yakin Ukiraniya kafar angulu ne, da kuma hana duk wata fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu.
Sai dai wannan ba shi ne batu mafi hatsari ba. Abinda ya jawo wa Trump jibin goshi shi ne, yadda shugaban da yake shirin barin ofishin ya dauki matakai irin wannan masu hatsari. Sakon shi ne cewa Trump da kuma hukumar cikin duhu, wacce Trump yake fada da ita a kodayaushe, suna daukar matakai tamkar za su cigaba da mulkin Amurka.
Wannan matakin yana kunshe da wasu abubuwa guda biyu, da dayansu yake a matsayin bala’i mai girma ga Trump.
Mene ne shi?
Wannan yana nufin cewa gwmanatin da take aiki a boye, tasirinta ya wuce cikin iyakar Amurka ya isa cikin nahiyar turai. Domin a lokaci daya tare da Amurkan su ka sanar da daukar mataki daya na fadada yaki a kan kasarRasha da zurfafa kai mata hari. Hakan yana nufin cewa yaki zai cigaba ba tare da kakkautawa ba ta yadda koda wani shugaban kasar ta Amurka ya zo ba zai iya tsayar da shi ba. Hakan za ta faru ne ta hanyar kai wa Rasha hari mai tsanani na tsokana da zai sa ita kuma ta yi ramuwa mai tsanani. Idan hakan ta faru, to Trump ba shi da wani zabi da zai hana shi cigaba da yaki.
Abu na biyu kuwa shi ne kokarin rusa shakshiyya dinsa da nuna cewa bai dace da shugabancin kasa kamar Amurka ba, da hakan zai iya sa a samar da wani yanayi da zai sa a kira yi sabon zabe a kasar da gwamnatin boye za ta sake dawowa ta cigaba da mulki.
Dukkanin wadannan abubuwan biyu masu yiyuwa ne. Yana kuma fahimtar abinda yanayin da yake zagaye da shi.
Watakila wannan ne ya sa tun yanzu Trump din yake tananta ganin Zlynisky ya mika kai ga dukkanin sharuddan Rasha na sulhu.
Shin Zelensky zai yi wa Trump Tawaye?
A birnin Paris Trump ya gana da shugaban Ukiraniya Zelensky na wasu ‘yan mintoci kadan, ya kuma fada masa sakon da yake so ya sani.
Bayan da ya koma birnin Kiev,ya yi maganganu masu jan hankali dake nuna amincewa da manufar Trump. Sai dai kuma bayan wani lokaci kadan ya aike da wani sakon wanda ya rusa na farko.
Abinda ya fada shi ne cewa ba da jimawa na zai tuntubi Biden domin ya yi maganar zaman kasarsa memba a cikin kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato. Domin a halin yanzu shi ne shugaban kasar Amurka. Ya kuma kara da cewa; Bai dace da hankali ba a ce ya yi Magana da Trump alhali bai kai ga zama shugaban kasa ba balle ya zama yana da tasiri.
Wannan zancen da Zelensky din ya yi, ya zama tamkar sukar Trump ce da wuka! Tana kuma nuni da cewa a matsayinsa na shugaban Ukiraniya tamkar yana jin cewa Trump ba zai yi shugabancin Amurka a karo na biyu ba.
Wannan ne ya sa Trump ya fito fili ya mayar da martani mai karfi cewa; Abu mafi hatsari da yake faruwa shi ne yadda Zelyenisky ya dauki mataki na wauta, ya kai wa Rasha hari da makami mai linzami.
Zelensky ya fadi haka ne a daidai lokacin da aka cimma wata yarjejniya ta boye da ta faru wacce ita ce, kawo karshen yakin Lebanon, shi kuma shugaban Syria ya mika mulki ba tare da zubar da jini ba, ya kuma tafi zuwa Rasha, Ita kuwa Rasha ta karbi Ukiraniya ta yadda za a kawo karshen yaki idan Trump ya zama shugaban kasa.
Sai dai kuma da akwai gibi da wannan yarjejeniyar take da ita. Ita ce cewa Rasha ce za ta sami babbar nasara, su kuma kasashen yammacin turai su yi asara mai girma. Domin girman matsayin yammacin kasar Ukiraniya ta fuskar muhimmanci bai kai na Syria ba. Musamman yadda a cikin shekarun bayan nan kasar ta Syria za ta zama fagen wasan kasashe da dama,musamman mai dai mutum irin Urdugan wanda ya kware wajen sauya salo da launi tamkar hawainiya. Tabbas yana yin haka ne akan manufofi masu muhimmanci a siyasance ga kasarsa.
Sanannen abu ne cewa tun a baya Rasha ta sha yi wa shugaban kasar ta Syria nasiha akan ya gana da Urdugan domin bude kafar tattaunawa da shi, da kuma mayar da alaka a tsakanin kasashen.
Sai dai bai yi hakan ba saboda wasu dalilai na kashin kai. Duk da cewa a zahiri ya sha fadin cewa, ba zai gaba da shugaban kasar da take mamaye da wani sashe na kasarsa ba. Sai idan ya janye ya fice daga Syria sannan zai zauna da shi.
A lokacin da Urdugan ya saki akalar masu dauke da makamai su ka nufi Halab, Rasha ta kasance a tsakiyar aiwatar da wannan shirin. Sai dai ita ma tabbas ba kanwar lasa ba ne,domin ta za ta saki dukkanin katunan da suke hannunta ba, domin ba ta amince da alkawullan Amurka ba, koda kuwa na Trump ne. Sai idan ya shiga cikin fadar White House ya kuma rike wani abu mai karfi a hannu.
Matsayar Amurka Akan Sabuwar Gwamnatin Syria
Minsitan harkokin wajen Syria ya bayyana rashin tabbacinsa akan cewa Julani zai kare tsiraru a cikin kasar Syria, duk kuwa da cewa ya ji maganganu masu dadi daga bakinsa.
Dama dai tun da fari, Washington ta bayyana cewa; Magankanu masu dadi suna fitowa daga bakin “Hay’atu Tahriruns-sham” amma ita Amurka ta fi son ganin aiki a kasa ba kalamai na baki ba.
Tabbas, abinda nufi a nan ba wai batu ne na tsiraru ba, abinda Amurkan take nufi, shi ne manufofinta. Ya za a kare mata manufofi a cikin Syria din.
Tare da cewa Amurkan ta sanar da Julani cewa ba za ta cigaba da maganar a kamo mata Julani ba, kuma ta janye dala miliyan 10 da ta sa a kansa, sai dai kuma a aikace ba za ta cire kungiyarsa daga cikin ta ‘yan ta’adda ba cikin gaggawa, domin ta cigaba da yi masa matsin lamba ya yi abinda take so.
A wajen yin hakan kuwa, babu abinda Amurkan ba za ya aikata ba da zai iya jefa kasashen yankin cikin hatsari.