Rundunar Sojin Isra’ila Ta Sanar Da Halakar Kanal A Rundunar Sojin Mamaya A Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da halakar kwamandan runduna ta 401 ta Isra’ila a wani harin kwantan bauna da aka kai musu a Gaza Kafofin

Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da halakar kwamandan runduna ta 401 ta Isra’ila a wani harin kwantan bauna da aka kai musu a Gaza

Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun rawaito cewa: Kwamandan rundunar sojin Kanar Ihsan Daksa, shi ne kanal na shida da ya halaka tun bayan fara yakin Zirin Gaza.

Rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da kashe Kanal Ihsan Daksa kwamandan bataliya ta 401 tare da raunata wani jami’i na daban a wani harin kwantan bauna da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka kai kan tawagar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a Zirin Gaza.

Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Tankar kwamandan bataliya ta 401 da wata tankar ta daban sun tarwatse sakamakon tashin nakiya da aka dasa a kan hanyarsu a yankin Jabaliya, lamarin da ya yi sanadin halakar jami’in sojan tare da raunata wani guda, yayin da kwamandan runduna ta 162 ya yanke shawarar nada Meir Biderman a matsayin kwamandan runduna ta 401, don maye gurbin Kanal din da aka kashe a Jabaliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments