A jiya Lahadi rundunar ta “Kassam” ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta bayyana cewa ta kai hari akan sojojin kasa na HKi a yankin “Shaima’a” dake arewacin Gaza, tare da kwantar da su kasa baki daya.
Bugu da kari sanarwar dakarun na “Kassam” ta kunshi cewa sun kai hari akan motar buldoza ta soja, ta hanyar amfani da makamin “ Yasin 105” da kuma bom din “Ra’adiyah” a kusa da masallacin Shahid “Imad Aqal” a arewacin Gaza.
A gefe daya sojojin HKI suna cigaba da tafka laifukan yaki akan al’ummar Gaza, ta hanyar yi musu kisan kare dangi da kuma jefa su cikin yunwa.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu babu wata rana daya da sojojin HKI ba su yi wa Falasdinawa kisan gilla. A yau ne dai yakin na Gaza yake cike kwanaki 402 da fara shi, da kawo yanzu ya ci rayukan mutane fiyar da 43,000, yayin da wasu da sun haura 100,000 su ka jikkata.