Mataimakin shugaban kasar Rasha ya sanar da cewa shugabannin kasashe 24 ne za su halarci taron koli na kasashen BRICS a Kazan.
Yuri Ushakov, ya sanar a wani taron manema labarai cewa, shugabannin kasashe 24 sun tabbatar da halartar taron na BRICS.
A bisa rahoton Pars Today da ya nakalto kafar yada labarai ta BRICS, adadin kasashen da za su halarci taron na iya karuwa, amma a halin yanzu wakilan kasahe 32 ne ake tabbacin halartarsu a taron.
Ya kuma kara da cewa wannan taro na iya zama babban taron koli kan manufofi da suka hada kasshen duniya a karkashin BRICS da aka taba gudanarwa a kasar Rasha.
A cewar Ushakov, shugabannin kasashen BRICS 9 ne za su halarci taron, wanda ke da manyan ajanda biyu: taron kasashe mambobin BRICS da ke mai da hankali kan “karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban don ci gaban duniya da tabbatar da adalci” da kuma tarurruka a karkashin tsarin BRICS+ wanda ke da manufa da taken: Gina Makomar Duniya Tare.”
Ya kuma ce a shekarar 2024, an gudanar da taruka sama da 20 daga cikinsu har da wadanda suka gudana a matakin ministoci.
Za a gudanar da taron na BRICS daga ranar 22 zuwa 24 ga Oktoba, 2024, a birnin Kazan na kasar Rasha, kuma an gayyaci wakilai daga kasashen Asiya, Afirka, Yammacin Asiya, da Latin Amurka a cikin tsarin BRICS+.
A halin yanzu, wannan kungiya tana da kasashe 10 da suka hada da Brazil, Rasha, Indiya, China, Afirka ta Kudu, Iran, Masar, Saudi Arabia, Habasha, da Hadaddiyar Daular Larabawa.
A watan Satumba shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da cewa kasashe 34 sun bayyana sha’awarsu ta shiga kungiyar BRICS domin zama mambobinta a hukumance.