Rasha ta yi Allah wadai da kisan Sayyed Hassan Nasrallah

Kakakin fadar Kremlin ta Rasha, Dmitry Peskov, ya yi Allah wadai da kisan babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, da kuma hare-haren da Isra’ila

Kakakin fadar Kremlin ta Rasha, Dmitry Peskov, ya yi Allah wadai da kisan babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, da kuma hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a yankunan da ke da yawan jama’a a kasar Lebanon, yana mai gargadin afkuwar  matsaloli na jin kai irin wanda aka gani a Gaza.

Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya ce kisan Sayyed Nasrallah ya haifar da “mummunan tashin hankali a yankin.”

Ya kara da cewa harin bama-bamai da aka kai a wuraren zama na jama’a a Lebanon ya haifar da hasarar rayukan mutane masu yawa, kuma zai haifar da wasu matsalolin na daban masu muni.

Tun daga farko na sanar da kisan Sayyid Nasrallah, ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar da bayani na yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa Nasrallah, tare da yin gargadin irin illar da take tatatre da hakan ga daukacin yankin gabas ta tsakiya.

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta kara da cewa, wannan ta’addancin na cike da munanan sakamako ga kasar Labanon da ma daukacin yankin, kuma Isra’ila ce za ta dauki cikakken alhakin dukkanin abin da zai ya biyo bayan hakan.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta “sake yin kira ga Isra’ila da ta gaggauta tsagaita wuta, wanda zai dakatar da zubar da jinin da ake yi, da kuma samar da yanayi na sasantawa a siyasance da bin hanyoyi na diplomasiyya.”

A wanann Litinin firaministan kasar Rasha Mikhail Mishustin ya isa birnin Tehran tare da wata babbar tawaga ta jami’an Rasha, inda zai gana da manyan jami’an gwamnatin kasar Iran akan batutuwa da suak shafi alakoki tsakanin kasashen biyu, da kuma halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments