Rasha Ta Musanta Rahotannin Cewa Putin Ya Tattauna Da Trump

Fadar Kremlin ta musanta rahotannin da ke cewa zababben shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna da shugaban kasar Vladimir Putin inda suka tattauna kan yakin

Fadar Kremlin ta musanta rahotannin da ke cewa zababben shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna da shugaban kasar Vladimir Putin inda suka tattauna kan yakin Ukraine.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce Putin ba shi da takamaiman shirin yin magana da Trump a halin yanzu, kuma rahotannin dake yawo ba gaskia ne ba, kamar yadda ya fadawa manema labarai.

Da aka tambaye shi ko Putin yana da shirye-shiryen tuntubar Trump, Peskov ya ce: “Babu wasu takamaiman tsare-tsare tukuna.”

Jaridar Washington Post ce ta fara bayar da rahoton cewa Trump ya yi hira ta wayar tarho da Putin daga yankin Mar-a-Lago da ke Florida a ranar Alhamis, kwanaki kadan bayan nasarar da ya samu a zaben da ya lashe a kan ‘yar takarar jam’iyyar Democrat Kamala Harris.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments