Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ya bayyana cewa, bangaren Rasha yana gargadin Isra’ila kan ko da wasa kada tunanin kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran.
Da yake zantawa da manema labarai a birnin Moscow, mataimakin ministan ya jaddada cewa illar yin hakan za ta shafi kowa.
Ryabkov ya kara da cewa: Mun sha yin gargadi, kuma har yanzu muna yin gargadi ga Isra’ila da kada ta saki ta tunanin yin hakan.
Ryabkov ya kara da cewa, Rasha na ci gaba da tuntubar Iran, ba tare da la’akari da irin yanayin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya ba.
Mataimakin ministan ya ci gaba da cewa: Muna ci gaba da tuntubar juna da bangaren Iran, kuma wadannan alakoki ba su da alaka da sauye-sauyen tsarin siyasa da kuma yanayin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya a halin yanzu.
Tun da farko, yayin wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin, ministan tsaron Haramtacciyar Kasar Isra’ila Yoav Galant bai janye yiwuwar kai hare-hare kan cibiyoyin samar da makamashin nukiliya na kasar Iran ba.
Gallant ya shaidawa CNN cewa: “Dukkan zabukan suna baje kan teburi.