Raisi: ‘Yan Sahayoniya Ba Su San Wani Abu Mai Suna ‘Yan’adamtaka Ba

Shugaban kasar ta Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa; Yanzu dukkanin duniya ta fahimci cewa, ‘yan sahayoniya masu aikata laifuka ba su aiki da

Shugaban kasar ta Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa; Yanzu dukkanin duniya ta fahimci cewa, ‘yan sahayoniya masu aikata laifuka ba su aiki da kowance irin ka’ida ta ‘yanadamtaka ko dokokin kasa da kasa.

Shugaban kasar na Iran ya bayyana haka ne dai a yayin tattaunawa ta wayr tarho da ya yi da takwaransa na kasar Syria, Basshar Assad, wanda ya yi masa jajen shahadar Birgediya janar Muhammad Riza Zahidi da wasu abokan aikinsa da HKI ta yi wa kisan gilla a birnin Damascuss.

Bugu da kari shugaban kasar ta Iran ya ce, lamari ne da babu shakku a cikinsa cewa, ‘yan sahayoniya da su ka tafka wannan ta’addancin da kuma masu goyon bayansu za su fuskanci sakamakon abinda su ka aikata.

Shugaban kasar ta Iran ya yi wa shugaban na Syria godiya akan taya juyayi da ya yi,sannan kuma ya kara da cewa; A kodayaushe  jamhuriyar musulunci ta Iran tare da Syria, suna bayyanawa duniya cewa; HKI  daidai take da cutar daji ,wacce take kawo cikas a tsaro da zaman lafiya a cikin wannan yankin da ma duniya.

Har ila yau shugaban kasar ta Iran ya yi kira ga kasashen wannan yankin da su kara kaimi wajen yin aiki tare domin fuskantar laifukan da ‘yan sahanoyar suke tafkawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments