Rahoto: Matasa kusan miliyan 2 ba su samu ilimi ko aiki ko wani horo ba a Ghana

Akalla matasa miliyan 1.9 ‘yan shekaru tsakanin 15 zuwa 35 a Ghana ne ba su samu ilimi ko aiki ko kuma wani horo ba (NEET),

Akalla matasa miliyan 1.9 ‘yan shekaru tsakanin 15 zuwa 35 a Ghana ne ba su samu ilimi ko aiki ko kuma wani horo ba (NEET), a cewar wani rahoton bincike kan kudaɗen shiga da iyali na shekarar 2023 da aka fitar.

Binciken, wanda Hukumar Kididdiga ta Ghana ta fitar, ya yi nuni da cewa mata ne su ke da adadi mafi yawa na mutum miliyan 1.2 yayin da maza su ke da adadin 715,691 a cikin matasan Ghana da ba su samu ilimi, aiki ko kuma wani horo ba, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Ghana GNA ya rawaito.

Kazalika rahoton ya bayyana cewa mutum ɗaya daga cikin matasa uku na NEET na zaune ne a babban birnin yankin Accra, inda matasa fiye da rabin miliyan (565,360) ba sa yin komai.

Baya ga Accra, akwai yankuna kamar Ashanti da yankin tsakiya da gabashi da kuma yammacin Ghana da adadin matasan da ba sa komai ya haura mutum 100,000.

A jumulla dai, mata suna wakiltar kashi 21.0 cikin 100 na matasan NEET, adadin da ya wuce kashi 1.5 cikin 100 da ke wakiltar maza.

Idan aka kwatanta da watanni ukun karshe na 2023 da na shekarar 2022, jimullar ragin da aka samu na matasan NEET ya kai maki 5.9 daga kashi 24.1 zuwa 18.2 cikin 100, inda aka samu ragin matasa kusan rabin miliyan (462,998).

A sauran yankuna 15 da ake da su a kasar ta Ghana kuwa, an samu ragin adadin matasa na NEET a jinsi biyu da ake da su, inda aka samu ragin kashi 5.9 a fannin maza sai kuma 0.3 cikin dari na ƙari a fannin mata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments