Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin wanda ya gabatar da jawabi a jiya Alhamis ya bayyana cewa, a halin yanzu sabon tsarin da zai tafiyar da duniya anan gaba yana kan ganiyar ginuwa.
Shugaba Putin ya kuma kara da cewa; Tsohon tsarin da ya tafiyar da duniya ya riga ya rushe, kuma a karkashin sabon tsari mai bangarori da yawa bai kamata wata al’umma ta zama an bar ta a baya ba.
Shugaban na kasar Rasha ya yi gagrgadi akan cewa abu ne mai yiyuwa kasashen turai su yi amfani da makaman Nukiliya, domin sun saba cin bulus, su aikata laifuka ba tare da sun fuskanci hukunci ba.
Wani sashe na jawabin shugaban kasar na Rasha ya kunshi taya Donald Trump murnar cin zaben shugabancin kasar Amurka, sannan ya kara da cewa Rasha a shirye take ta yi aiki da duk wani shugaba da al’ummar Amurka ta zabe shi.
Har ila yau Vladimir Putin ya ce, a lokuta da dama kasarsa ta takawa masu son mamaye duniya birki kuma tana cigaba da yin haka.
Shugaban kasar ta Rasha ya kuma ce, ba kasarsa ce ta fara amfani da karfi ba, amma kuma idan bukatar amfani da karfi ta taso, to tabbas za ta yi.
Dangane da takunkuman da kasashen turai su ka kakaba wa Rasha, Vladimir Vladimir ya ce, Abinda su ka so yi shi ne mayar da Rasha saniyar ware a duniya, to amma hakan bai yiyu ba, saboda duniya tana da bukatuwa da Rasha.