Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadin cewa gwamnatin Isra’ila za ta fuskanci mummunan martani idan ta yi gigin kai wa kasar Lebanon hari.
Sabon shugaban na Iran ya yi wannan gargadin ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a ranar Litinin.
Pezeshkian ya bayyana tsananin damuwarsa kan yadda tashe-tashen hankula ke kara kamari a kan iyakar kudancin Lebanon da yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye.
Ana ci gaba da zaman dar-dar tsakanin Isra’ila da kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta Lebanon bayan wani harin roka da ya yi sanadin mutuwar mutane 12 tare da jikkata wasu 40 a garin Majdal Shams da ke yankin tuddan Golan na kasar Syria da Isra’ila ta mamaye.
Yayin da Isra’ila ta zargi Hizbullah da kai harin, kungiyar ta Hizbullah ta musanta dukkan zarge-zargen karya game da hakan.
Tun bayan faruwar lamarin, ana ci gaba da yin musayar wuta a kan iyakar kasar Lebanon da yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye.
A ranar jiya Litinin ne dai gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai wani sabon farmaki kan kasar Labanon da sunan mayar da martani kan kungiyar Hizbullah.
Ana fargabar cewa Isra’ila za ta yi amfani da hakan a matsayin hujjar kai wani gagarumin farmaki kan Lebanon.
A nasa bangaren, Macron ya bayyana fatan cewa Iran za ta inganta dangantakarta da Faransa da sauran kasashen Turai a lokacin mulkin Pezeshkian.