Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga kungiyoyin gwagwarmaya, sannan kuma ya yaba da irin rawar da suke takawa a kasashen Labanon da Palastinu, yayin ganawarsa da mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem da Sakatare Janar na kungiyar Islamic Jihad, Ziad Al-Nakhalah, a ziyarar da suka kai Jamhuriyar Musulunci ta Iran, domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasar Iran.
A yayin ganawarsa da Sheikh Qassem, Pezeshkian ya jaddada cewa, goyon bayan matakin tsayin daka wani aiki ne halastacce kuma daya daga cikin muhimman manufofin kasar Iran, inda ya kara da cewa karfafa alaka da kasashen musulmi na daga cikin abubuwan da gwamnatinsa ta sa gaba.
Ya kuma yaba da irin jaruntakar da kungiyar Hizbullah ta nuna kan hare-haren yahudawan sahyoniya, ya kuma yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila aikatawa a kan Falasdinawa, “wadanda ake aiwatar da su tare da goyon bayan Amurka,” ya kuma dauke su a matsayin abin kunya a goshin masu da’awar kare hakkin dan Adam.”
Ya kuma yi kira ga kasashen musulmi da su hada kai, wanda idan har aka cimma hakan, “Sahyoniyawa ba za su kuskura su aikata munanan laifuka a kan Falastinawa da ma sauran kasashen musulmi ba.”
A nasa bangaren, Sheik Qassim ya jaddada cewa, da ba don goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, dab a a cimma nasarorin da aka samu ba a kan Isra’ila, yana mai jaddada cewa, sakamakon tsayin daka da jajirtattun al’ummar Gaza suka yi, za a sake samun wata babbar nasara da yardar Allah.
A daya bangaren kuma, shugaban na Iran ya jaddada a yayin ganawarsa da Al-Nakhalah cewa, wannan taron yana dauke da wani muhimmin sako ga masu neman nisantar da Iran daga yunkurin gwagwarmaya.
Ya jaddada cewa matsayin Iran kan batun Palastinu da goyon bayan da take ba wa ‘yantar da birnin Kudus ba zai canja ba ta hanyar sauya gwamnatoci, yana mai cewa “babu wani abu da zai hana mu ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar al’ummar falastinu da masu taimakon falastinawa.”
A nasa bangaren, Al-Nakhalah ya yaba da ganawarsa da shugaban kasar Iran, yana mai jaddada cewa wadannan tarurrukan suna dauke da muhimman sakonni ga yankin da ma duniya baki daya.