Pezeshkian: Iran da Indonesiya suna taka gagarumar rawar  wajen hadin kan musulmi

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce fadada alaka tsakanin Iran da Indonesia a fannoni daban-daban zai taimaka wajen samar da hadin kai tsakanin al’ummar

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce fadada alaka tsakanin Iran da Indonesia a fannoni daban-daban zai taimaka wajen samar da hadin kai tsakanin al’ummar musulmi da kuma samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya aikewa shugaban kasar Indonesia Joko Widodo a yau  Juma’a, inda ya bayyana murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai na kasar Indonesia, wanda ke tunatar da zagayowar ranar ayyana ‘yancin kai a kasar a ranar 17 ga watan Agustan shekarar 1945.

Ya yi ishara da alakar tarihi da kuma batutuwan da suka shafi moriyar juna tsakanin Tehran da Jakarta da kuma irin karfin da suke da shi a bangarori daban-daban, ya kuma bayyana fatan bangarorin biyu za su kara habaka dangantakar kud da kud da abota ta dindindin.

Kasashen Iran da Indonesiya sun neman karfafa alakarsu ta siyasa da tattalin arziki a daidai lokacin da ake ci gaba da tada jijiyoyin wuya a duniya.

A cikin watan Mayu, manyan jami’an Iran da Indonesia sun rattaba hannu kan takardu da yarjejeniyoyin 11 don karfafa hadin gwiwa.

Bisa yarjejeniyar, Tehran da Jakarta za su inganta hadin gwiwa a fannonin cinikayya , soke biza, musayar al’adu, sa ido kan kayayyakin magunguna, kimiyya da fasaha gami da mai da iskar gas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments