Pezeshkian: dangantakar Tehran da Moscow na kara karfi a dukkanin bangarori

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, dangantaka tsakanin Iran da Rasha tana karfi a dukkanin bangarori. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a ganawarsa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, dangantaka tsakanin Iran da Rasha tana karfi a dukkanin bangarori.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a ganawarsa da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, a gefen taron kasa da kasa na “Hadin kai zaman lafiya da ci gaba, a ka gudanar birnin Ashgabat na kasar Turkmenistan.

A yayin ganawar, shugabannin biyu sun yi musayar ra’ayi kan fadada dangantakar kasashensu ta fuskar tattalin arziki da al’adu.

Pezeshkian ya bayyana jin dadinsa da damar ganawa da takwaransa na Rasha, ya kuma kara da cewa dangantakar tattalin arziki da al’adu tsakanin kasashen biyu na kara karfi.

Ya kara da cewa, tare da kudurin shugabannin kasashen biyu, dole ne a ci gaba da kara yin hadin gwiwa tsakanin Iran da Rasha.

Ya ce Iran da Rasha suna alfahari da karfin hadin gwiwa da kuma tallafawa junansu.

Har ila yau, ya bayyana fatan ganin an gaggauta kammala yarjejeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin bangarorin biyu, yana mai cewa, yana fatan kammala yarjejeniyar a yayin taron koli na kasashen BRICS da za a yi a kasar Rasha a  cikin ‘yan makonni masu zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments