Iran ta ce za ta tattauna da kasashen turai – Faransa, Jamus da Birtaniya – kan batutuwan da suka shafi shirin nukiliyarta.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya bayyana cewa, mataimakan ministocin harkokin wajen Iran da na kasashen Turai uku da ake kira E3 za su gana a ranar Juma’a.
Ya sake jaddada matsayin Iran kan mu’amala da hadin gwiwa da sauran kasashe bisa mutunci, hikima da moriyar juna.
Ya bayyana cewa taron da za a yi da kasashen Turai uku zai kasance ci gaba da tattaunawar da aka yi da kasashen uku a watan Satumba a gefen taron shekara-shekara na MDD a birnin New York.
Kakakin na Iran ya ce, za a tattauna batutuwa da dama da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa da suka hada da batutuwan Falasdinu da Lebanon da kuma batun nukiliya.
A ranar alhamis din da ta gabata ne dai hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta IAEA ta kasashe 35 ta amince da wani kuduri da kungiyar tarayyar turai ta gabatar da cewa Tehran ba ta da wani mummunan hadin gwiwa da hukumar tare da neman a samar da wani cikakken rahoto kan ayyukanta na nukiliya kafin lokacin bazara na 2025.