Najeriya: NLC Ta Bukaci Gwamtai Da Ta Gaggauta Janye Karin Farashin Man Fetur

Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), ta gargadi Gwamnatin Tarayya da ta yi gaggauta janye karin farashin man fetur da ta yi. An wayi gari a

Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), ta gargadi Gwamnatin Tarayya da ta yi gaggauta janye karin farashin man fetur da ta yi.

An wayi gari a ranar Talata a sassan kasar nan da karin farashin litar man fetur, inda ake sayar da shi Naira 855, zuwa 897 daga Naira 568 kan kowace lita.

Sai dai cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukan sada zumunta, NLC ta yi kira ga gwamnati da ta mayar da farashin yadda yake a da.

“Muna kira da a janye karin farashin mai da aka yi a sassan kasar nan ba tare da bata lokaci ba.”

Karin farashin na zuwa ne yayin da ake fama da matsalar karancin mai a fadin kasar.

Kazalika, karin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da kamfanin NNPC ya yi korafin cewa ana bin sa makudan kudade da suka kai Dala biliyan shiga na kudin masu shigo da mai.

Sai dai Gwamnatin Tarayya, ta musanta bai wa kamfanin NNPC umarnin da ya kara farashin mai.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan Mai, Sanata Heineken Lokpobiri, ya nesanta gwamnatin da bayar da umarnin karin.

“Muna Allah-wadai da wannan ikirari da ba shi da tushe bare makama, wanda yunkuri ne na fusata jama’a,” in ji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments